ZABE: INEC na bukatar ma�aikata 15, 545 a Kwara, miliyan 1.2 a Najeriya>>Yakubu Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC, ta ce za ta tura ma�aikatan gudanar da zabe har 15, 545 a jihar Kwara domin gudanar da zaben 2019. Kwamishinan Zabe na Tarayya da ke Jihar Kwara, Garba Attahiru Madami ne ya bayyana haka a Ilorin babban birnin jihar. Ya ce ana bukatar ma�aikatan wucin-gadi 13, 199 da za su yi aikin gudanar da zaben Shugaban Kasa da na Majalisar Tarayya. Sauran sun hada da jami�an zaben na dindindin. Sannan kuma ya ce za a tura masu bautar kasa, wato NYSC har 7, 567 domin gudanar da zaben. A wani jikon kuma, Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana cewa INEC ta na bukatar akalla jami�an gudanar da zabe da jami�an tsaro a kalla milyan 1.2 domin gudanar da zaben 2019 a fadin kasar nan. Yakubu ya bayyana hakan ne a Kano, inda ya jaddada cewa INEC na bukatar akalla jami�an tsaro 360 da za su kula da rumfunan zabe a lokacin da ake gudan...