Posts

Showing posts with the label wasanni

Portugal za ta kwace lambar yabo mafi girma da ta baiwa Ronaldo

Image
Portugal za ta kwace lambar yabo mafi girma da ta baiwa Ronaldo Shugaban Portugal Marcelo Rebelo de Sousa, ya ce gwamnatinsa tana nazari kan yiwuwar kwace babbar lambar yabo da ta baiwa dan wasan kasar Cristiano Ronaldo. Matakin a cewar shugaba Rebelo de Sousa, na da nasaba da hukuncin biyan tara da kotun Spain ta yanke kan Ronaldo, bayan samunsa da laifin kin biyan haraji, yayin da yake wasa a kungiyar Real Madrid. A shekarar 2016 Portugal ta karrama Ronaldo da lambar yabo mafi girma da ake baiwa farar hula ta �Portuguese Order of Merit� a turance, bayan taimakawa kasar da ya yi, wajen lashe gasar cin kofin kasashen nahiyar Turai. Sai dai a ranar Talatar da ta gabata, wata kotun Spain ta yanke hukuncin tilasatawa Cristiano Ronaldo biyan Dala miliyan 3 da dubu 57 saboda kin biyan makudan kudade na haraji ga gwamnatin kasar. Da fari hukuncin kan Ronoldo na daurin shekaru 2 biyu ne a gidan Yari amma aka sassauta hukuncin zuwa biyan tarar euro dubu 365 na take, tare da biyan karin euro mi...

Man City ta fi kowa cin kwallaye a Turai

Image
Manchester City ta zama ta farko da ta zura kwallo sama da 100 a tsakanin manyan kungiyoyin da ke buga gasar Lik-Lik ta Turai ta kakar 2018/19. A ranar Lahadi City ta ci Huddersfield 3-0 a wasan mako na 23 a gasar Premier, kuma Danilo ne ya fara cin kwallo, wadda ita ce ta 100 da ta zura a raga a dukkan fafatawa da ta yi a bana. Daga baya ne ta kara biyu a karawar ta hannun Raheem Sterling da kuma wadda Leroy Sane ya ci, jumulla City tana da kwallo 102 da ta zura a raga a wasannin da ake yi. 'Yan wasa 17 ne suka ci wa City kwallo 102 a kakar bana, inda Sergio Aguero da Gabriel Jesus kowanne ya ci 14, sai Sterling mai 12 da kuma Sane wanda ya ci 11. Tun bayan da Crystal Palace da Leicester City suka yi nasara a kan City a Premier, kawo yanzu ta dura kwallo 22 a raga a wasa hudu da ta buga. A kakar 2013/14 City ta lashe kofin Premier ta kuma zura kwallo 156 a karkashin jagorancin Manuel Pellegrini a dukkan gumurzun da ta yi a kakar. Paris Saint-Germain ce ke biye da City a yawan cin ...