Posts

Showing posts with the label Labarai

Majalisar tarayya ta tabbatar da dubu 30 mafi karancin Albashi

Image
Majalisar tarayya ta tabbatar da dubu 30 mafi karancin Albashi Majalisar wakilai ta tabbatar da Naira dubu 30 a matsayin mafi karancin Albashi a kasarnan, majalisar ta tabbatar da hakanne a zaman da ta yi na yau, Talata inda hakan ya saba da dubu 27 da majalisar koli ta aminta dashi. Zaman majalisar wanda kakakin majalisar, Yakubu Dogara ya jagoranta, ya bayyana cewa sun amincene da rahoton wani kwamiti da suka kafa akan mafi karancin Albashin sannan sun yi la'a kari da irin halin matsin da ake ciki a kasarnan wajan daukar wannan mataki. Yanzu dai za'a mikawa majalisar dattijai wannan kudiri dan ta tabbatar dashi, a cikin kudirin me kamfani ko wata ma'aikata da yawan ma'aikatan da yake biya albashi basu kai mutum 25 ba baya cikin wannan tsari na biyan mafi karancin Albashi.

An Tura Mayaka Mata Domin Fatattakar Boko Haram

Image
An Tura Mayaka Mata Domin Fatattakar Boko Haram Rundunar Sojojin Sama ta Kasa, NAF ta bada sanarwar tura zaratan sojojin sama mata da ake kira Mata Zaratan Yaki zuwa yankin Arewa maso Gabas domin yin gumurzu da Boko Haram. Babban Hafsan Hafsoshin Sama, Sadique Abubakar ya ce a yanzu haka akwai da dama da ke gwabza yaki tare da zaratan musamman a wurare daban daban. Ya shaida wa PRNigeria cewa NAF babu ruwanta da nuna bambanci, kuma ta na kara cicciba kowane jinsi domin ya samu karin horo da goguwar kwarewa a aikin sa. � Mu na kiran su da suna Mata Zaratan Yaki ne saboda sun horu, sun gogu kuma sun samu kwarewa wajen iya gwabza gumurzun fada a duk inda aka kai su, ko kuma inda suka samu kan su. � Su ma wadannan matan kamar abokan aikin su maza su ke. Sun kware sosai wajen kakkabe abokan gaba masu ta�adda musamman wajen iya kai farmaki daga sama, tare da bada dauki ga sojojin da ke gumurzu da Boko Haram a kasa. Ya ce sun samu horo a cikin Najeriya da kuma kasashen Turai.

HAKO MAN FETUR: Jihar Bauchi Na Dab Da Zama Kamar Jihohin Niger Delta

Image
HAKO MAN FETUR: Jihar Bauchi Na Dab Da Zama Kamar Jihohin Niger Delta Nan gaba kadan da yardar Allah jihar Bauchi ita ma za ta zamo kamar jihohin Niger Delta masu arzikin man fetur. Wadannan hotuna da kake gani 'kari ne game da rahotannin da muke kawo muku game da kokarin da Shugaba Buhari yake yi don raya kasar mu musamann Arewa, aikin tonon rijiyoyin mai a kauyen Kolmari dake karamar hukumar Alkaleri, cikin jihar Bauchi. Hakika akwai jin dadi ga 'yan kasar nan cikin shekaru kadan masu zuwa in sha Allah. Rariya.

Najeriya ta gargadi kasashen ketare kan yi mata katsalandan

Image
Najeriya ta gargadi kasashen ketare kan yi mata katsalandan Gwamnatin Najeriya ta gargadi kasashen ketare da su kaucewa yin katsalandan kan al�amuran da suka shafi kasar, wanda ka iya haifar da rudani, rashin yadda da juna tsakanin �yan Najeriya, da kuma haifar da shakku kan sahihancin zabukan kasar. Gargadin na kunshe cikin sanarwar da kakakin gwamnatin Najeriyar Malam Garba Shehu ya fitar a Abuja. Gwamnatin Najeriya dai ta maida martani ne kan tsokacin da wasu kasashen ketare da suka hada da Amurka Birtaniya da kuma kungiyar EU suka yi, kan matakin shugaban kasar Muhammadu Buhari, na dakatar da Alkalin Alkalai mai shari�a Walter Onnoghen, tare da nada Mai shari�a Ibrahim Tanko a matsayin mukaddashi. Sanarwar ta yi amfani da kakkausan harshe wajen sukar duk wani yunkurin yin katsalandan kan al�amuran Najeriya da kai iya rura wutar sabani tsakanin �yan kasar ko kuma haddasa rashin yadda da tsarin dimokaradiyar da take kai. Majalisar dattijan Najeriya dai, ta tsaida Talata mai zuwa, a m...

ZABE: INEC na bukatar ma�aikata 15, 545 a Kwara, miliyan 1.2 a Najeriya>>Yakubu

Image
ZABE: INEC na bukatar ma�aikata 15, 545 a Kwara, miliyan 1.2 a Najeriya>>Yakubu Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC, ta ce za ta tura ma�aikatan gudanar da zabe har 15, 545 a jihar Kwara domin gudanar da zaben 2019. Kwamishinan Zabe na Tarayya da ke Jihar Kwara, Garba Attahiru Madami ne ya bayyana haka a Ilorin babban birnin jihar. Ya ce ana bukatar ma�aikatan wucin-gadi 13, 199 da za su yi aikin gudanar da zaben Shugaban Kasa da na Majalisar Tarayya. Sauran sun hada da jami�an zaben na dindindin. Sannan kuma ya ce za a tura masu bautar kasa, wato NYSC har 7, 567 domin gudanar da zaben. A wani jikon kuma, Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana cewa INEC ta na bukatar akalla jami�an gudanar da zabe da jami�an tsaro a kalla milyan 1.2 domin gudanar da zaben 2019 a fadin kasar nan. Yakubu ya bayyana hakan ne a Kano, inda ya jaddada cewa INEC na bukatar akalla jami�an tsaro 360 da za su kula da rumfunan zabe a lokacin da ake gudan...

Za a hade Facebook Whatsapp da Instagram wuri daya

Image
Za a hade Facebook Whatsapp da Instagram wuri daya Kamfanin Facebook ya bayyana shirinsa na hade shafin da kuma Whatsapp da Instagram duka wuri daya. Wannan zai bada dama ga masu amfani da shafukan daban-daban su rika zumunta ko tura sakwanni ko da kuwa mutum yana da rajista da manhaja daya zai iya zumunta da wadanda ke amfani da sauran. Misali, idan mutum yana amfani da Facebook, sai abokinsa yana amfani da Instagram kadai, za su iya zumunci ko tura sako tsakaninsu. Shafukan da ke zaman kansu, hadewarsu zai sa a rika tura sakwanni tsakaninsu. Facebook dai shaidawa BBC cewa wannan shirin da sauran aiki a gaba domin yanzu aka fara. Jaridar New York Times ce ta fara wallafa wannan labarin kuma ana sa ran cewa mai kamfanin na Facebook Mark Zuckerberg ne ya fito da wannan sabon tsarin. Kamar yadda jaridar ta New York times ta wallafa, an riga an fara wannan aikin kuma ana sa ran za a kamala shi zuwa karshen wannan shekara ko kuma farkon shekara mai zuwa. BBChausa.

Cikin Kwanaki 15 Zan Gama Da Shari'ar Barayin Tattalin Arzikin Kasa>>Inji Sabon Alkalin Alkalai Na Kasa

Image
Cikin Kwanaki 15 Zan Gama Da Shari'ar Barayin Tattalin Arzikin Kasa>>Inji Sabon Alkalin Alkalai Na Kasa Sabon babban Alkalin Alkalai na Nijeriya (CJN) Mai shari'a Ibrahim Tanko Muhammad ya ce daga yanzu duk wata shari'a da ake yin ta a kotu wacce take da nasaba da cin hanci da rashawa, ya yi alkawarin za'a kammalata a yanke hukunci a tsakanin kwanaki goma sha biyar kacal. Rariya.

Anyo abin yin waya cikin mutane ba tare da sunji abinda kake cewa ba

Image
Anyo abin yin waya cikin mutane ba tare da sunji abinda kake cewa ba An kirkiri wani abin yin waya wanda baya fitar da sautin murya, koda kuwa kana cikin mutane zaka iya yin wayarka ba tare da kowa ya ji abinda kake cewa ba. Cheddar ta ruwaito cewa, an kirkiri abinne asali dan ma'aikata dake yawan magana a gurin aikinsu ta yanda zasu iya yin waya ba tare da sun takurawa abokan aikinsu da surutu ba. Saidai rahoton yace wannan abu ya kasa dan kuwa bai samar da abinda ake so ba.

Shugaba Buhari ya dakatar da alkalin alkalai, Walter Samuel Nkanu Onnoghen ya nada Ibrahim Tanko Muhammad rikon kwarya

Image
Shugaba Buhari ya dakatar da alkalin alkalai, Walter Samuel Nkanu Onnoghen ya nada Ibrahim Tanko Muhammad rikon kwarya Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya dakatar da alkalin alkalan Najeriya, Walter Samuel Nkanu Onnoghen wanda ake tuhuma a kotu bisa zargin rashin bayyana kadarorinshi sannan ya nada Mr. Ibrahim Tanko Muhammed a matsayin Alkalin alkalan Najeriya me rikon kwarya.

Kalli yanda wata mata ke faffallawa jariri mari

Image
Kalli yanda wata mata ke faffallawa jariri mari Wasu mutanen dai tausayinsu da sauki, jariri irin wannan da ko Allah be dora mai alkalami ba ko laifin me yayi da zai cancanci wannan muzgunawa? Wani hoton bidiyo me tayar da hankali ya bayyana a shafukan sada zumunta inda aka ga wata baiwar Allah na faffalawa jariri mari. Hannun baiwar Allahn kawai ake gani a cikin bidiyon me dauke da Dayis ne ko kunshi?  Tana dukan yaron, a yayin da ya fara kuka kuma sai ta rufe mai baki kamar zata kasheshi, wannan abu ya harzuka da dama daga cikin wanda suka kalli bidiyon inda aka rika kira da a yadashi da kyau ko za'a iya gano ko wacece. Ba ma wai dukan da ta wa jaririn kadaine abin takaici ba, irin yanda bin ya mata dadi har ta dauki hoton bidiyo take watsawa Duniya. Allah shi kyauta.

Ashe ba'a zuwa kasuwa da da tsaleliyar mace? karanta abinda ya faru da wannan da ya shiga kasuwa da antinshi

Image
Ashe ba'a zuwa kasuwa da da tsaleliyar mace? karanta abinda ya faru da wannan da ya shiga kasuwa da antinshi Wani ma'abocin shafin Twitter ya dauki hankulan mutane sosai bayan da ya bayar da labarin shigar kasuwar da yayi kasuwa tare da Antinshi, yace, na biya ta kasuwa da antina, sai tace, kai ya zaka kawoni nan? An gayama ana zuwa kasuwa da tsaliliyar mace. Ya dauki hoton antin tashi tana zaune cikin mota yayin da wani me KekeNapep/ Adaidaita sahu ke kare mata kallo, hakan ya dauki hankulan mutane sosai.

Za'a samu Kisifewar Wata gobe Litinin

Image
Za'a samu Kisifewar Wata gobe Litinin Hukumar kula da sararin samaniya, NASRDA ta hannun me magana da yawunta, Felix Alle ta bayyana cewa za'a samu kusufin wata a gobe, Litinin idan Allah ya kaimu. Kisifewar watan zata farune da misalin karfe 4 na daren litinin sannan zai yi sauki da misalin karfe shida akamar yanda sanarwar ta bayyana.

Kalli hotunan 10yearchallenge na wasu musulmai da suka koma Kiristoci

Image
Kalli hotunan 10yearchallenge na wasu musulmai da suka koma Kiristoci Wannan wani mutum ne wanda a da musulmi ne kuma ya bayyana kanshi a matsayin me fafutukar Jihadi, sunanshi Muhammad amma yanzu ya bayyana cewa ya koma Kirista, ya bayyana hakane a shafinshi na dandalin sada zumunta inda ya saka hoton shekaru 10 da suka gabata lokacin yana musulmi da na yanzu.  Hakanan itama wannan ta kasa wadda yanzu ke amfani da sunan Destiny ta bayyana cewa da ita musulmace amma yanzu ta koma Kirista ta kuma saka hotunan ta a da wanda lokacin tana musulma da kuma na yanzu.