ZABE: INEC na bukatar ma�aikata 15, 545 a Kwara, miliyan 1.2 a Najeriya>>Yakubu
ZABE: INEC na bukatar ma�aikata 15, 545 a Kwara, miliyan 1.2 a Najeriya>>Yakubu
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC, ta ce za ta tura ma�aikatan gudanar da zabe har 15, 545 a jihar Kwara domin gudanar da zaben 2019.
Kwamishinan Zabe na Tarayya da ke Jihar Kwara, Garba Attahiru Madami ne ya bayyana haka a Ilorin babban birnin jihar.
Ya ce ana bukatar ma�aikatan wucin-gadi 13, 199 da za su yi aikin gudanar da zaben Shugaban Kasa da na Majalisar Tarayya.
Sauran sun hada da jami�an zaben na dindindin.
Sannan kuma ya ce za a tura masu bautar kasa, wato NYSC har 7, 567 domin gudanar da zaben.
A wani jikon kuma, Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana cewa INEC ta na bukatar akalla jami�an gudanar da zabe da jami�an tsaro a kalla milyan 1.2 domin gudanar da zaben 2019 a fadin kasar nan.
Yakubu ya bayyana hakan ne a Kano, inda ya jaddada cewa INEC na bukatar akalla jami�an tsaro 360 da za su kula da rumfunan zabe a lokacin da ake gudanar da zabuka a ko�ina cikin kasar nan.
Shugaban na INEC ya yi wannan bayani ne ta bakin Sa�ad Idris, Shugaban Cibiyar Zabe ta Kasa da ya wakilce shi.
An shirya taron ne a Kano domin sanin makamar aiki lokacin zabe ga jami�an tsaro.
Tare da hadin guiwar Cibiyar Tallafa wa Zabuka ta Kungiyar Tarayya Turai aka shirya taron.
Kasancewa Najeriya na da masu jefa kuri�a har milyan 84, Yakubu ya ce Najeriya ce ta biyu a yawan masu jefa kuri�a a kasar da ake dimokradiiya a duniya.
Yakubu ya hori jami�an tsaro su yi aiki tsakanin su da Allah kamar yadda doka ta tanadar domin a tabbar da samun ingantacce, sahihi kuma karbabbe.
Premiumtimeshausa.

Comments