Ku Zabi Mai Gaskiya Da Rikon Amana, Cewar Sheikh Bala Lau
Ku Zabi Mai Gaskiya Da Rikon Amana, Cewar Sheikh Bala Lau Shugaban Kungiyar Jama'atu Izalatul Bidi'a Wa Ikamatus Sunnah na kasa Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya bukaci jama'ar Najeriya da su duba Mutum mai gaskiya da rikon amana su zabe shi a matsayin Shugaban Kasa, a babban zaben dake tafe. Sheikh Lau ya cigaba da cewar, babban abinda ake nema a Shugabanci shine gaskiya da rikon amana a wajen Shugaba, dukkanin Shugaban da aka san shi da kamanta gaskiya da rikon amana shine Shugaban da ya dace Jama'a su zaba, kuma lallai Jama'a su guji dukkanin shugaba wanda yayi kaurin suna ta fuskar cin amana da rashin gaskiya. Malamin yayi wannan kira ne lokacin da yake zantawa da manema labarai a Gidanshi dake Kaduna dangane da batun zabe da ya kunno kai. Imam Bala Lau ya kuma yi nasiha ga dukkanin 'yan takara musanman na Shugaban Kasa da cewar su amince da sakamakon zabe da Hukumar zabe zata fadi, domin hakan zai taimaka wajen samar da zaman lafiya a kasa, da dorewar shi kansh...