Posts

Hoton Hadiza Gabon da ya birge

Image
Hoton Hadiza Gabon da ya birge Tauraruwar fina-finan Hausa, Hadiza Gabon kenan a wannan hoton nata da ta sha kyau, tubarkallah, muna mata fatan Alheri.

[WAKA] Hamisu Breaker -Alaka

Image
Sabuwar wakar Hamisu breaker mai suna � Alaka � wannan wakar ta musammance domin nishadantar da masoya da yan soyayya. GA KADAN DAGA BAITIN WAKAR:- � Yanayi yazo gareni � Nima yazo gareni � Ki daure ki kulani � Nima sai ka kulani � Alakarmu dake take sanya rai ya fahimta� Yanayi yazo gareni � Nima yazo gareni � Ki daure ki kulani � Nima sai ka kulani � Alakarmu dake take sanya rai ya fahimta � Nasan yanayin da zai zam alkairee � Alakarmu dakai taso na baka komai dozin � Bakon yanayinmu zaya zam akairee � Nashirya farin cikinki zan nemowa � Kosun tsara akanki zan rushewa Audio Player 00:00 00:00 Use Up/Down Arrow keys to increase or decrease volume. DOWNLOAD HERE

[ALBUM] Nura M Inuwa -Mai Zamani

Image
Sako Daga Nura M Inuwa Kan Sabon Album dinsa Alhamdulillahi Rabbil Alameen!Tabbas duk abun da aka sakawa lokaci zaizo ya wuce har ya zama tarihi.Muna qara godiya ga Allah S.W.T daya nuna mana wannan rana,sannan muna qara godiya ga masoya dangane da qoqarin da sukeyi wajen bibiya da yi mana fatan alkhairi har ma da hakurin jiran da sukeyi kafin albums su pito kasuwa. Ina amfani da wannan dama na shedawa masu saurararo cewa a yau Laraba 23-01-2019 albums din Ango da Mai zamani sun pita kasuwa. Zaku iya samu a duk wata kasuwar CD ko wajen masu siyar da CD.Kuma ina yiwa masu sauraro albishir cewa zasu ji sababbin abubuwa wadanda suka hada da Fadakarwa,Nishadi,Soyayya da kuma Wasa kwakwalwa.Muna yiwa kowa fatan alkhairi, Allah ya barmu tare cikin kaunar Juna,Ameen.

Tsarin Trade Moni salon sayen kuri'ane da wayau>>Transparency International

Image
Tsarin Trade Moni salon sayen kuri'ane da wayau>>Transparency International Kungiyar kula da rashawa da cin hanci ta Transparency International ta bayyana cewa tsarinnan na Trade Moni da gwamnatin shugaban kasa, Muhammadu Buhari ke bayarwa ga kananan 'yan kasuwa a Najeriya sayen kuri'ane da wayau. Shugaban kungiyar, Awwal Rafsanjani ne ya bayyana haka a wata hira da yayi da gidan talabijin na Channels, Awwal ya bayyana cewa tsarin sayen kuri'ane da wayau inda gwamnatin tarayya ke amfani da kudin baitilmani tana bayarwa. Yace dalilinsu na cewa haka shine cikin shekaru 3 da suka gabata karkashin mulkin APC bata kawo wannan tsari ba sai ana gab da yin zabe, ya kara da cewa koda kuwa ba salon sayen kuri'a bane da wayau dole Duniya zata kalleshi a haka.

Na Tabbata Da Umaru Musa Yar'adua Na Da Rai Da Jam'iyyar APC Zai Yi Saboda Adalcinta>>Hajia Bilkisu Kaikai

Image
Na Tabbata Da Umaru Musa Yar'adua Na Da Rai Da Jam'iyyar APC Zai Yi Saboda Adalcinta>>Hajia Bilkisu Kaikai Tsohuwar Mai ba tsohan Gwamna Ibrahim Shehu Shema shawara akan ilmin 'yaya mata, wadda ta dawo jamiyyar APC Hajiya Bilkisu Kaikai, ta bayyana cewa sakamakon irin ayyukan alherai da Kuma gina kasa da shugaban kasa Muhammadu Buhari, da Gwamna Masari ke Yi a jihar Katsina. Ta ce da Allah yasa Marigayi tsohan shugaban kasa malam Umaru Musa Yar'adua yana da rai da yanzu yana cikin jamiyyar APC. Hajiya Bilkisu Kaikai ta bayyana haka ne a Karamar Hukumar Kusada a wajen taron gangamin yakin neman zaben Gwamna Aminu Bello Masari da yake yi a shiyyar Daura. Bilkisu Kaikai ta cigaba da cewa duk wannan matsaloli na rashin tsaro da kasar nan ke fuskanta, Jamiyyar PDPce ta asassa shi da gangan. Yanzu Kuma shugaba Buhari da Gwamna Masari suna yin bakin kokarin su domin kawo karshen fitinu, don hakamu mu ma al'umma my cigaba da yin addua samun dawamamme zaman lafiya a ka...

Bilkisu Shema 'Yar kwalisa

Image
Bilkisu Shema 'Yar kwalisa Jarumar fina-finan Hausa, Bilkisu Shema kenan a wannan hoton nata data sha kyau, tubarkallah, muna mata fatan Alheri.

Tsakanin Maryam Booth da wata da tace mata yawan kwalliya yana sa tsufa

Image
Tsakanin Maryam Booth da wata da tace mata yawan kwalliya yana sa tsufa Tauraruwar fina-finan Hausa, Maryam Booth ta saka wannan hoton nata a shafinta na sada zumunta kuma masoyanta da dama sun yaba, saidai wata ta gayamata cewa, Salam yawan yin kwalliyar zamani yana tsufar da mutum, ki kula. Saidai Maryam din ta bata amsar cewa, Anan Hanyar cin abincina yake.

Shugaba Buhari ya dakatar da alkalin alkalai, Walter Samuel Nkanu Onnoghen ya nada Ibrahim Tanko Muhammad rikon kwarya

Image
Shugaba Buhari ya dakatar da alkalin alkalai, Walter Samuel Nkanu Onnoghen ya nada Ibrahim Tanko Muhammad rikon kwarya Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya dakatar da alkalin alkalan Najeriya, Walter Samuel Nkanu Onnoghen wanda ake tuhuma a kotu bisa zargin rashin bayyana kadarorinshi sannan ya nada Mr. Ibrahim Tanko Muhammed a matsayin Alkalin alkalan Najeriya me rikon kwarya.

Matsalar dake tsakanin Shugaba Buhari da Obasanjo

Image
Daga Shafin Abubakar A Adam babankyauta Babu yadda Za,ayi Azauna inuwa guda tsakanin Adalin Shugaban Najeriya Muhammadu buhari da Tsohon Shugaban Najeriya Cif Olusegun obasanjo Acikin Najeriya Domin Adalin Shugaban Najeriya Muhammadu buhari Shine Mutun Na farko dake yaki da Chin hanchi da Rashawa Acikin Najeriya A karkashin Mulkin Dimokaradiya janhoriya ta uku Acikin Najeriya baki daya Shi kuma tsohon Shugaban Najeriya Cif Olusegun Obasanjo Shine Mutun Na farko da yakawo Chin hanchi da Rashawa karkashin Mulkin Dimokaradiya jangoriya ta uku Acikin tarihin Najeriya Kamar yadda Muka Sani ne Lokacin da Obasanjo yazama Shugaban Najeriya 1999 karkashin Mulkin Dimokaradiya janhoriya ta uku baida Naira dubu dari tashi ta kan Shi domin Hatta kayan da Obasanjo yayi yakin Zabe dasu IBB ne ya siyammai su Amma yau Obasanjo Shine ya Mallaki biliyoyin daloli Acikin Najeriya Domin idan kuka kalli iya gidan gonan Obasanjo dake Otta kunsan Akwa dukiyar Alummar Najeriya Aciki Tsabar Daura Najeriya Akan t...

Kalli yanda wata mata ke faffallawa jariri mari

Image
Kalli yanda wata mata ke faffallawa jariri mari Wasu mutanen dai tausayinsu da sauki, jariri irin wannan da ko Allah be dora mai alkalami ba ko laifin me yayi da zai cancanci wannan muzgunawa? Wani hoton bidiyo me tayar da hankali ya bayyana a shafukan sada zumunta inda aka ga wata baiwar Allah na faffalawa jariri mari. Hannun baiwar Allahn kawai ake gani a cikin bidiyon me dauke da Dayis ne ko kunshi?  Tana dukan yaron, a yayin da ya fara kuka kuma sai ta rufe mai baki kamar zata kasheshi, wannan abu ya harzuka da dama daga cikin wanda suka kalli bidiyon inda aka rika kira da a yadashi da kyau ko za'a iya gano ko wacece. Ba ma wai dukan da ta wa jaririn kadaine abin takaici ba, irin yanda bin ya mata dadi har ta dauki hoton bidiyo take watsawa Duniya. Allah shi kyauta.

Buhari yayi kokari amma bazai iya ci gaba ba ya je gida ya huta>>PDP

Image
Buhari yayi kokari amma bazai iya ci gaba ba ya je gida ya huta>>PDP Jam'iyyar PDP ta bayyana cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari yayi kokari amma yanzu be da kuzarin ci gaba da mulki dan haka ya kamata ya je gida ya huta. Shugaban jam'iyyar Uche Secondus ne ya bayyana haka a wajan yakin neman zaben jam'iyyar, jiya a Kaduna, Secondus yace sake zaben Buhari kamar baiwa wasu boyayyun mutanene dama su ci gaba da juya kasarnan yanda suka ga dama domin ba Buharin ne ke mulki ba. Ya bukaci a zabi Atiku dan ya samar da ayyukan yi da kawar da yunwa. Shima Atikun da yake jawabi yace, APC ta yi Alkawarin habbaka tattalin arzikin kasarnan lokacin da ta karbi Mulki amma ba'a gani a kasa ba sannan ta yi Alkawarin samar da tsaro amma duk gashinan sai kashe-kashe ake samu.

Idan zaka kara aure gani ina jira>>Wata ta tallata kanta ga Atiku

Image
Idan zaka kara aure gani ina jira>>Wata ta tallata kanta ga Atiku Bayan da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya saka wasu hotunan yakin neman zabenshi da yayi a Kaduna inda yake nuna farun cikinshi, jama'a da dama masoyanshi sun bayyana farin cikinsu, ita kuwa wata ta tallata kantane ga Atikun. Matashiyar me suna, Cecilia ta bayyana wa Atikun cewa, lallai taro yayi taro, Ranka ya dade idan zaka kara aure, gani fa.

Fati K.K ta haskaka a wannan hoton

Image
Fati K.K ta haskaka a wannan hoton Tauraruwar fina-finan Hausa, Fati K. K kenan a wannan hoton nata da ta haskaka, tubarkallah tasha kyau, muna mata fatan Alheri.

INEC ta ce Oby ta makara: Sai an yi zabe da ita

Image
INEC ta ce Oby ta makara: Sai an yi zabe da ita Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya, INEC ta ce 'yar takarar shugabancin kasar a jam'iyyar ACPN Obiageli Ezekwesili ta makara wajen janye takararta a zaben 2019. Mai magana da yawun hukumar, Malam Aliyu Bello ya ce sashe na 35 na dokar zabe ta shekarar 2010, ya nuna cewa jam'iyya ko dan takara zai iya janye takararsa kwanaki 45 kafin ranar da za a kada kuri'a. Ya ce a zaben 2019, hukumar INEC ta ware 17 ga watan Nuwamba a matsayin rana ta karshe da 'yan takarar shugabancin kasa da na majalisar za su iya janyewa. Malam Aliyu ya ce tanadin dokar shi ne idan dan takara ya yi niyyar janyewa daga takararsa, sai ya ankarar da jam'iyyarsa ta hanyar rubuta wasika inda ita kuma jam'iyyar za ta sanar da hukumar zaben. Ya ce jam'iyyar ACPN ba ta sanar da hukumar INEC ba a kan lokaci, don haka hukumar za ta ci gaba da shirye-shiryenta na zabe yadda ya kamata. Oby Ezekwesili dai ta janye daga takarar shugabancin Naj...

Mazaje na rububin auren matar da mijinta ya sake ta saboda tace Buhari zata zaba

Image
Mazaje na rububin auren matar da mijinta ya sake ta saboda tace Buhari zata zaba Ga dukkan alamu matarnan da mijinta ya saketa dalilin dagewa da ta yi akan sai ta zabi shugaban kasa, Muhammadu Buhari a zabe me zuwa ba zata yi kwantai ba domin kuwa yanzu haka an samu mazaje sun yunkuro da cewa zasu aureta, duk da cewa dai wasu sun bayyana rashin kyautawar abinda ta wa mijin nata da shima hukuncin da ya dauka. Babban masoyin Shugaban Kasa a jihar Kano Auwal G Danbarno ya sha alwashin auren matar da mijinta ya sake saboda ta dage sai ta zabi Buhari.  Ya wallafa a shafinsa na facebook cewa, "Zan aureta ko ta kai shekaru ?ari, kuma ko kuturwa ce. Matar da mijinta ya sake ta kan za?en Buhari" Haka kuma shima wani da yake bayyana ra'ayinshi akan labarin da BBC suka wallafa ya bayyana cewa a shirye yake ya auri matar idan ta kammala Idda.

SIYASA BA DA GABA BA: Gwamna Tambuwal na Sakkawato ya karbi shugaba Buhari a filin jirgi

Image
SIYASA BA DA GABA BA: Gwamna Tambuwal na Sakkawato ya karbi shugaba Buhari a filin jirgi Gwamna Tambuwal ya karbi Shugaban Kasa, Muhammad Buhari a filin jirgin saman kasa da kasa na Sarkin Musulmi Abubakar Na Uku, a lokacin da ya isa jihar Sokoto domin yakin neman sake zaben shi karo na biyu a jihohin Sokoto da Kebbi, inda Shugaban kasa ya samu kyakkyawar tarbo ga dinbin mutanen da suka fito suna sai Baba, kafin ya wuce zuwa fadar mai Alfarma Sarkin Musulmi inda ya kai ziyara ta musammam.  Rariya

Zan Mayarwa Da Atiku Mota Da Kudaden Da Ya Ba Ni Domin Yi Masa Yakin Neman Zabe>>Rabi'u Biyora

Image
Zan Mayarwa Da Atiku Mota Da Kudaden Da Ya Ba Ni Domin Yi Masa Yakin Neman Zabe>>Rabi'u Biyora "Zai kasance babban kuskure gare ni na cigaba da amfani da motar da aka bani don na yi kamfen, tunda dai na bayyana cewa ba zan yi kamfen din ba. Hatta 'yan kudaden kashewar da aka bani duk suna nan a lissafe kuma zan mika su in sha Allah zuwa gobe. Ba zai yiwu in hana mutane hasashe akan wannan lamari ba, sai dai dole akwai cikakkiyar gaskiyar lamarin da ni Biyora na sani suma wadanda suka bani daga gidan dana koma a kwanakin baya suka sani. Na yanke shawarar dawowa tafiyata ta baya ne saboda wasu dalilan da nake ganin ta haka ne kawai zan fi samun saukin gudanar da rayuwata, koda kuwa naci gaba da yawo akan babur dina ne, tuni na saka an gyara mun shi don cigaba da zirga zirga akansa kamar yadda na saba a baya. Kalubale dole na sake fuskantarsa a yanzu kamar yadda na fuskanta a baya kila ma ya fi na baya yawa. In sha Allah bayanai za su fito ta yadda kowa zai fahimci dali...

Ashe ba'a zuwa kasuwa da da tsaleliyar mace? karanta abinda ya faru da wannan da ya shiga kasuwa da antinshi

Image
Ashe ba'a zuwa kasuwa da da tsaleliyar mace? karanta abinda ya faru da wannan da ya shiga kasuwa da antinshi Wani ma'abocin shafin Twitter ya dauki hankulan mutane sosai bayan da ya bayar da labarin shigar kasuwar da yayi kasuwa tare da Antinshi, yace, na biya ta kasuwa da antina, sai tace, kai ya zaka kawoni nan? An gayama ana zuwa kasuwa da tsaliliyar mace. Ya dauki hoton antin tashi tana zaune cikin mota yayin da wani me KekeNapep/ Adaidaita sahu ke kare mata kallo, hakan ya dauki hankulan mutane sosai.

Man City ta fi kowa cin kwallaye a Turai

Image
Manchester City ta zama ta farko da ta zura kwallo sama da 100 a tsakanin manyan kungiyoyin da ke buga gasar Lik-Lik ta Turai ta kakar 2018/19. A ranar Lahadi City ta ci Huddersfield 3-0 a wasan mako na 23 a gasar Premier, kuma Danilo ne ya fara cin kwallo, wadda ita ce ta 100 da ta zura a raga a dukkan fafatawa da ta yi a bana. Daga baya ne ta kara biyu a karawar ta hannun Raheem Sterling da kuma wadda Leroy Sane ya ci, jumulla City tana da kwallo 102 da ta zura a raga a wasannin da ake yi. 'Yan wasa 17 ne suka ci wa City kwallo 102 a kakar bana, inda Sergio Aguero da Gabriel Jesus kowanne ya ci 14, sai Sterling mai 12 da kuma Sane wanda ya ci 11. Tun bayan da Crystal Palace da Leicester City suka yi nasara a kan City a Premier, kawo yanzu ta dura kwallo 22 a raga a wasa hudu da ta buga. A kakar 2013/14 City ta lashe kofin Premier ta kuma zura kwallo 156 a karkashin jagorancin Manuel Pellegrini a dukkan gumurzun da ta yi a kakar. Paris Saint-Germain ce ke biye da City a yawan cin ...

Rabi'u Biyora Ya Dawo Tafiyar Buhari

Image
Rabi'u Biyora Ya Dawo Tafiyar Buhari Ga abinda ya rubuta ASSALAM ALAIKUM AL'UMMA... Sako Na Musammam  Da farko ina mika godiya mara iyaka a gareku tare da fatan Allah ya cigaba da yimana jagora a rayuwarmu gaba daya... Ina son amfanin da wannan dama na tunasar damu abun da muka sani tun tini dangane da yanayin siyasar wannan kasa (Nigeria), a tsakankaninmu yara, matsakaita da manyan mu ta yadda mafi akasari kan nemawa kansu bangaren siyasar da suke kyautata zaton zasu samu damar gudanar da ayyukansu da cikar burukansu ba tare da samun tsaiko ba.... Kusan sati uku kenan ana tattaunawa akan yanayin siyasar da Biyora ya samu kansa a cikinta, bayan da labari ya bayyana cewa na canza sheka zuwa tsagin gidan Alhaji Atiku Abubakar, bayan sanin da akayimun a bangaren tafiyar Baba Buhari, wannan abu ya janyo maganganu masu yawa musammam ga wadanda suke zaton kamar hakan bazai taba faruwa ba, wasu kuwa har gobe sun kasa aminta da cewa zan iya rabuwa da Baba Buhari a siyasance, duk da cew...