Posts

Entertainment

Image
Go to admin Thank you for visiting my website

Hacker

Image
Go  

Majalisar tarayya ta tabbatar da dubu 30 mafi karancin Albashi

Image
Majalisar tarayya ta tabbatar da dubu 30 mafi karancin Albashi Majalisar wakilai ta tabbatar da Naira dubu 30 a matsayin mafi karancin Albashi a kasarnan, majalisar ta tabbatar da hakanne a zaman da ta yi na yau, Talata inda hakan ya saba da dubu 27 da majalisar koli ta aminta dashi. Zaman majalisar wanda kakakin majalisar, Yakubu Dogara ya jagoranta, ya bayyana cewa sun amincene da rahoton wani kwamiti da suka kafa akan mafi karancin Albashin sannan sun yi la'a kari da irin halin matsin da ake ciki a kasarnan wajan daukar wannan mataki. Yanzu dai za'a mikawa majalisar dattijai wannan kudiri dan ta tabbatar dashi, a cikin kudirin me kamfani ko wata ma'aikata da yawan ma'aikatan da yake biya albashi basu kai mutum 25 ba baya cikin wannan tsari na biyan mafi karancin Albashi.

An Tura Mayaka Mata Domin Fatattakar Boko Haram

Image
An Tura Mayaka Mata Domin Fatattakar Boko Haram Rundunar Sojojin Sama ta Kasa, NAF ta bada sanarwar tura zaratan sojojin sama mata da ake kira Mata Zaratan Yaki zuwa yankin Arewa maso Gabas domin yin gumurzu da Boko Haram. Babban Hafsan Hafsoshin Sama, Sadique Abubakar ya ce a yanzu haka akwai da dama da ke gwabza yaki tare da zaratan musamman a wurare daban daban. Ya shaida wa PRNigeria cewa NAF babu ruwanta da nuna bambanci, kuma ta na kara cicciba kowane jinsi domin ya samu karin horo da goguwar kwarewa a aikin sa. � Mu na kiran su da suna Mata Zaratan Yaki ne saboda sun horu, sun gogu kuma sun samu kwarewa wajen iya gwabza gumurzun fada a duk inda aka kai su, ko kuma inda suka samu kan su. � Su ma wadannan matan kamar abokan aikin su maza su ke. Sun kware sosai wajen kakkabe abokan gaba masu ta�adda musamman wajen iya kai farmaki daga sama, tare da bada dauki ga sojojin da ke gumurzu da Boko Haram a kasa. Ya ce sun samu horo a cikin Najeriya da kuma kasashen Turai.

Shaye-shaye ko neman kananan yara za'ayi da kudin>>Teema Makamashi ta mayar da martani akan kudin da Ummi Zeezee tace abokan aikinta sun cinye

Image
Bayan da taurruwar fina-finan Hausa, Ummi Zeezee ta caccaki wasu daga cikin abokan aikinta akan cinye kudin da ta yi zargin sun yi wanda tace dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar ya bayar a rabawa 'yan Kannywood, abokiyar aikinta, Teema Makamashi ta mayar da martani me ban mamaki. Teema ta baiwa Ummi amsar cewa, Wallahi ba abinda zai musu karshema shanye kudin za ayi a shaye shaye ko kuma anemi yara kanana da kudin azzalumai kawai. Wannan dai ya jawo wasu na tambayar cewa kada kudi yasa su rika tonawa abokan sana'arsu asiri.

Ku Zabi Mai Gaskiya Da Rikon Amana, Cewar Sheikh Bala Lau

Image
Ku Zabi Mai Gaskiya Da Rikon Amana, Cewar Sheikh Bala Lau Shugaban Kungiyar Jama'atu Izalatul Bidi'a Wa Ikamatus Sunnah na kasa Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya bukaci jama'ar Najeriya da su duba Mutum mai gaskiya da rikon amana su zabe shi a matsayin Shugaban Kasa, a babban zaben dake tafe. Sheikh Lau ya cigaba da cewar, babban abinda ake nema a Shugabanci shine gaskiya da rikon amana a wajen Shugaba, dukkanin Shugaban da aka san shi da kamanta gaskiya da rikon amana shine Shugaban da ya dace Jama'a su zaba, kuma lallai Jama'a su guji dukkanin shugaba wanda yayi kaurin suna ta fuskar cin amana da rashin gaskiya. Malamin yayi wannan kira ne lokacin da yake zantawa da manema labarai a Gidanshi dake Kaduna dangane da batun zabe da ya kunno kai. Imam Bala Lau ya kuma yi nasiha ga dukkanin 'yan takara musanman na Shugaban Kasa da cewar su amince da sakamakon zabe da Hukumar zabe zata fadi, domin hakan zai taimaka wajen samar da zaman lafiya a kasa, da dorewar shi kansh...

Ummi Zeezee ta bayyana manyan 'Barayin Kannywood 5' bayan da ta zargesu da cinye kudin da Atiku ya bayar a rabawa 'yan Kannywood

Image
Ummi Zeezee ta bayyana manyan 'Barayin Kannywood 5' bayan da ta zargesu da cinye kudin da Atiku ya bayar a rabawa 'yan Kannywood Tauraruwar fina-finan Hausa, Ummi Zeezee ta yiwa wasu daga cikin abokan sana'arta kaca-kaca akan wasu kudi da tace dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar ya bayar a rabawa 'yan Kannywood masu yinshi amma suka raba kudin tsakaninsu. Abokan aikin nata da ta kira fitattun barayi 5 na Kannywood sune, Sani Musa Danja, Fati Muhammad, Zaharadeen Sani, Buhari Alamin da me bayar da umarni, Eemrana. A cikin wani zungureren rubutu da tayi a shafinta na sada zumunta tace taso ta dauresu akan wannan abu amma mahaifiyarta ta hanata tace ta barsu da Allah. Ga abinda tace kamar haka: � Zuwa ga Fati Mohd, Sani Danja, Zaharaddeen Sani, Al�amin Buhari and director eemrana�. � A ranar JUMA�AR data gabata mai girma dan takaran shugaban kasa ta jam�iyar PDP Alhaji atiku Abubakar ya shirya wani taro da zaiyi da yan fim da kuma mawaka na kannywood dan g...

HAKO MAN FETUR: Jihar Bauchi Na Dab Da Zama Kamar Jihohin Niger Delta

Image
HAKO MAN FETUR: Jihar Bauchi Na Dab Da Zama Kamar Jihohin Niger Delta Nan gaba kadan da yardar Allah jihar Bauchi ita ma za ta zamo kamar jihohin Niger Delta masu arzikin man fetur. Wadannan hotuna da kake gani 'kari ne game da rahotannin da muke kawo muku game da kokarin da Shugaba Buhari yake yi don raya kasar mu musamann Arewa, aikin tonon rijiyoyin mai a kauyen Kolmari dake karamar hukumar Alkaleri, cikin jihar Bauchi. Hakika akwai jin dadi ga 'yan kasar nan cikin shekaru kadan masu zuwa in sha Allah. Rariya.

KALLI ALJANIN DA AKE TUNAIN YA HALARCI TARON KWANKWASIYYA

Image
KALLI ALJANIN DA AKE TUNAIN YA HALARCI TARON KWANKWASIYYA Wata halitta da jama'a suke tunanin Aljani ne ya bayyana cikin suffar dattijo 'WAI' ya sauko daga sararin samaniya a kan keke, lokacin da ake taron Kwankwasiyya a karamar hukumar Birni. Da mutane suka tambaye shi, me ya kawo ka? Sai yace "Nazo ne domin naga Kwankwaso" Sarauniya.

Rahama Sadau ta kammala karatun jami'a

Image
Rahama Sadau ta kammala karatun jami'a Tauraruwar fina-finan Hausa,Rahama Sadau ta kammala karatun jami'ar da take yi a Cyprus wanda ta samu shaidar kallama karatu daga jami'ar Eastern Mediterranean, Rahamar ta bayyana hakane a shafukanta na sada zumunta inda tace kamin a kammala kamar ba za'a gama ba. Muna tayata murna da fatan Allah ya sawa karatu Albarka.

Najeriya ta gargadi kasashen ketare kan yi mata katsalandan

Image
Najeriya ta gargadi kasashen ketare kan yi mata katsalandan Gwamnatin Najeriya ta gargadi kasashen ketare da su kaucewa yin katsalandan kan al�amuran da suka shafi kasar, wanda ka iya haifar da rudani, rashin yadda da juna tsakanin �yan Najeriya, da kuma haifar da shakku kan sahihancin zabukan kasar. Gargadin na kunshe cikin sanarwar da kakakin gwamnatin Najeriyar Malam Garba Shehu ya fitar a Abuja. Gwamnatin Najeriya dai ta maida martani ne kan tsokacin da wasu kasashen ketare da suka hada da Amurka Birtaniya da kuma kungiyar EU suka yi, kan matakin shugaban kasar Muhammadu Buhari, na dakatar da Alkalin Alkalai mai shari�a Walter Onnoghen, tare da nada Mai shari�a Ibrahim Tanko a matsayin mukaddashi. Sanarwar ta yi amfani da kakkausan harshe wajen sukar duk wani yunkurin yin katsalandan kan al�amuran Najeriya da kai iya rura wutar sabani tsakanin �yan kasar ko kuma haddasa rashin yadda da tsarin dimokaradiyar da take kai. Majalisar dattijan Najeriya dai, ta tsaida Talata mai zuwa, a m...

Kannywood Atiku zata zaba>>Yakubu Muhammad

Image
Kannywood Atiku zata zaba>>Yakubu Muhammad Taurarron fina-finan Hausa, Yakubu Muhammad ya bayyana cewa, masana'antar Kannywood dan takarar shugaba kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar zata zaba saboda suna fatan zai tallafa musu idan ya zama shugaban kasa. Yakubu Muhammad ya bayyana hakane a wajan wani taro na musamman da wakilan Atiku Abubakar suka yi na jin ra'ayin jama'a a Kaduna, kamar yanda Punch ta ruwaito. Yakubu yace suna yin fina-finai marasa inganci wanda matsalar rashin shugabanci na gari ne ya jawo hakan. Sannan a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan zai iya tuna cewa, ya bayar da tallafin miliyan 200 ga masana'antun nishadantarwa. Dan haka Atiku zasu yi.

ZABE: INEC na bukatar ma�aikata 15, 545 a Kwara, miliyan 1.2 a Najeriya>>Yakubu

Image
ZABE: INEC na bukatar ma�aikata 15, 545 a Kwara, miliyan 1.2 a Najeriya>>Yakubu Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC, ta ce za ta tura ma�aikatan gudanar da zabe har 15, 545 a jihar Kwara domin gudanar da zaben 2019. Kwamishinan Zabe na Tarayya da ke Jihar Kwara, Garba Attahiru Madami ne ya bayyana haka a Ilorin babban birnin jihar. Ya ce ana bukatar ma�aikatan wucin-gadi 13, 199 da za su yi aikin gudanar da zaben Shugaban Kasa da na Majalisar Tarayya. Sauran sun hada da jami�an zaben na dindindin. Sannan kuma ya ce za a tura masu bautar kasa, wato NYSC har 7, 567 domin gudanar da zaben. A wani jikon kuma, Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana cewa INEC ta na bukatar akalla jami�an gudanar da zabe da jami�an tsaro a kalla milyan 1.2 domin gudanar da zaben 2019 a fadin kasar nan. Yakubu ya bayyana hakan ne a Kano, inda ya jaddada cewa INEC na bukatar akalla jami�an tsaro 360 da za su kula da rumfunan zabe a lokacin da ake gudan...

Za a hade Facebook Whatsapp da Instagram wuri daya

Image
Za a hade Facebook Whatsapp da Instagram wuri daya Kamfanin Facebook ya bayyana shirinsa na hade shafin da kuma Whatsapp da Instagram duka wuri daya. Wannan zai bada dama ga masu amfani da shafukan daban-daban su rika zumunta ko tura sakwanni ko da kuwa mutum yana da rajista da manhaja daya zai iya zumunta da wadanda ke amfani da sauran. Misali, idan mutum yana amfani da Facebook, sai abokinsa yana amfani da Instagram kadai, za su iya zumunci ko tura sako tsakaninsu. Shafukan da ke zaman kansu, hadewarsu zai sa a rika tura sakwanni tsakaninsu. Facebook dai shaidawa BBC cewa wannan shirin da sauran aiki a gaba domin yanzu aka fara. Jaridar New York Times ce ta fara wallafa wannan labarin kuma ana sa ran cewa mai kamfanin na Facebook Mark Zuckerberg ne ya fito da wannan sabon tsarin. Kamar yadda jaridar ta New York times ta wallafa, an riga an fara wannan aikin kuma ana sa ran za a kamala shi zuwa karshen wannan shekara ko kuma farkon shekara mai zuwa. BBChausa.

Idan dai kunji dadin mulkin Buhari to ku sake zabenshi>>Atiku

Image
Idan dai kunji dadin mulkin Buhari to ku sake zabenshi>>Atiku Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya bukaci 'yan Najeriya dasu sake zaben shugaban kasa, Muhammadu Buhari a zabe me zuwa muddin dai sun ji dadin mulkin na Buhari. Atikun ya bayyana hakane a wata sanarwa da ya fitar ta hannun me magana da yawunshi, Phrank Shuaibu inda yace, a duk fadin Duniya babu inda ake samun shugaban kasa da bai tabuka abin arziki ga 'yan kasa ba amma kuma ya fito yana so a sake zabarshi. Yace shugaba Buhari kara saka Najeriya yayi cikin matsala a mulkinshi kuma kasashen Duniya dama 'yan Najeriya sun yi ittifakin cewa bazai ci zaben da za'a yi ba saboda 'yan Najeriya sama da miliyan dari basa iya cin abinci koda sau daya a rana dan haka suna cikin yunwa kuma suna fushi dashi, ba zasu saka mishi kuri'a ba. Vanguard ta ruwaito cewa, Atikun ya kara da cewa,  ga duk wanda yasan ya samu aikin yi a karkashin gwamnatin Buhari to ya zabi Buharin wanda kuw...

Ban yi Allah wadai da dakatar da alkalin alkalai ba>>A'isha Buhari

Image
Ban yi Allah wadai da dakatar da alkalin alkalai ba>>A'isha Buhari Uwargidan shugaban kasa, Hajiya A'isha Buhari ta karyata wasu labarai dake watsuwa a shafukan sada zumunta cewa wai ta yi Allah wadai da dakatarwar da mijinta, shugaban kasa, Muhammadu Buhari yawa alkalin alkalai na kasa. Hajiya A'isha ta hannun me magana da yawunta, Sulaiman Haruna ta bayyana cewa ba ta yi magana akan dakatar da alkalin alkalan ba kuma ta yi kira ga masu watsa cewa ta yi maganar da su daina daga yanzu.

Cikin Kwanaki 15 Zan Gama Da Shari'ar Barayin Tattalin Arzikin Kasa>>Inji Sabon Alkalin Alkalai Na Kasa

Image
Cikin Kwanaki 15 Zan Gama Da Shari'ar Barayin Tattalin Arzikin Kasa>>Inji Sabon Alkalin Alkalai Na Kasa Sabon babban Alkalin Alkalai na Nijeriya (CJN) Mai shari'a Ibrahim Tanko Muhammad ya ce daga yanzu duk wata shari'a da ake yin ta a kotu wacce take da nasaba da cin hanci da rashawa, ya yi alkawarin za'a kammalata a yanke hukunci a tsakanin kwanaki goma sha biyar kacal. Rariya.

Anyo abin yin waya cikin mutane ba tare da sunji abinda kake cewa ba

Image
Anyo abin yin waya cikin mutane ba tare da sunji abinda kake cewa ba An kirkiri wani abin yin waya wanda baya fitar da sautin murya, koda kuwa kana cikin mutane zaka iya yin wayarka ba tare da kowa ya ji abinda kake cewa ba. Cheddar ta ruwaito cewa, an kirkiri abinne asali dan ma'aikata dake yawan magana a gurin aikinsu ta yanda zasu iya yin waya ba tare da sun takurawa abokan aikinsu da surutu ba. Saidai rahoton yace wannan abu ya kasa dan kuwa bai samar da abinda ake so ba.

Ya Allah ka zaba mana wanda yafi zama Alheri tsakanin Buhari da Atiku>>Kumurci

Image
Ya Allah ka zaba mana wanda yafi zama Alheri tsakanin Buhari da Atiku>>Kumurci Tauararon fina-finan Hausa, Shu'aibu Lawal, Kumurci, wanda yana daya daga cikin taurarin fina-finan Hausa wanda ke bayan Atiku, yayi wata addu'a da ta dauki hankulan mutane, inda yace idan Buhari ne Alheri, Allah ya bashi idan kuma Atiku ne Alheri Allah ya canja mana ya bashi. Gadai abinda ya rubuta kamar haka: BISMILLAHI ALLAH kazaba mana shugaba nagari mubamusan komaiba, Allah sai abinda kasanar damu, idan baba buhari Alkairine Allah kabashi idan kuma ba Alkairi bane to Allah ka gaggauta canjashi kabawa baba Atiku idan shidin alkarine ga wannan kasa tamu Allah ka amsa dan karfin mulkinka da son Annabi (S A W) SUBHANAKA LA ILMU LANA ILLA MA ALLAMTANA INNAKA ANTAL ALIMUN HAKIM

Biyora ya samu kyautar mota bayan da ya mayar da Atiku wadda ya bashi

Image
Biyora ya samu kyautar mota bayan da ya mayar da Atiku wadda ya bashi Sanannen me kare muradun shugaban kasa,Muhammadu Buhari a shafukan sada zumunta wanda ya koma goyon bayan Atiku na dan wani lokaci, har aka bashi kyautar mota, sannan daga baya ya dawo bayan Buhari ya kuma mayarwa da Atiku motar da aka bashi, ya koma hawan babur dinshi da ya saba, yanzu dai an bashi kyautar wannan motar Da ake ganin hotonta a sama. Biyoran ya bayyana a shafinshi cewa an shirya mai wata walima ta musamman ta dawowa jam'iyyar APCn da yayi sannan aka bashi kyautar wannan motar.